Jam’iyar PDP ta bayyana cewa tunda ya dawo daga jinya a birnin London, yanzu shugaban kasa Muhammad Buhari, yana da cikakkiyar lafiyar da zai iya jagorancin Najeriya.
Buhari ya dawo Najeriya a ranar Asabar, bayan da yabar gida tun ranar 7 ga watan Mayu don yin jinya a birnin London.
A wata sanarwa da mai magana da yawun PDP na kasa Dayo Adeyeye, yafitar, jam’iyar tayi murna da dawowar shugaban kasar ta kuma godewa Allah da yabashi lafiya.
Ta kuma yi addu’ar Allah yakarawa shugaban kasar lafiya domin ya fitar da tattalin arzikin Najeriya daga mawuyacin halin da yake ciki.
” Muna da yakinin cewa yanzu mai girma shugaban kasa yana da cikakkiyar lafiyar cigaba da gudanar da aikinsa a matsayinsa na shugaba,” sanarwar tace.
“Mun godewa Allah da ya ceci rayuwarsa.
“Muna addu’ar Allah yakara masa lafiya da kuma fahimtar yadda zai ceto tattalin arzikin mu daga mawuyacin halin da yake ciki da kuma kawowa yan Najeriya saukin wahalhalun da suke fuskanta.”