Za a fara ne da yin alwala tare da rokon Allah da siffofinSa daga nan sai a karanta wadannan Ayoyin AlKur’ani a bayyane akan wanda aka yi wa Sihirin;
1) Ayatul Kursiyyu ( Suratul Bakara: Aya ta 255
2) Shahidallahu ( Suratul Imran: Aya ta 18
Daga nan sai a nemi ganyen Magarya kunne bakwai, a dan daka su da Dutse sannan a saba dandakakken ganyen da ruwa, sai a zuba cikin bukitin wanka. Daga nan sai a karanta wadannan Ayoyin AlKur’ani a cikin ruwan;
* A’uzubillahi Minas Shaidanin Rajim
* Ayatul Kursiyyu
* ‘ Wa’auhaina,,,,,” Suratul A’araf: Aya ta 110 zuwa 117
* ” Wakala Fir’auna…” Suratul Yunus: Aya ta 79 zuwa 82
* ” Kalu ya Musa….” Suratul Daha: Aya ta 65 zuwa 70
* Suratul Kafirun
* Suratul Ikhlas
* Suratul Falak
* Suratul Nas
* Sai a karanta ” La’ilaha Illallahu Wahdahu Lasharikalahu Lahul Mulku Walahulhamdu Wahuwa Ala Kulli Shai’in Kasiri” ( Sau Dari). Sai a kammala da Salatin Manzon Allah ( SAW)
Daga sai a dibi ruwan a ba mara lafiyan ya sha sai kuma ya yi wanka da sauran ruwan.
Allah ne mafi sani.