Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo,yace yan Najeriya da yawa suna farin ciki da dawowar shugaban kasa Muhammad Buhari.
Ya fadi haka ne lokacin da yakewa yan jaridun fadar shugaban kasa jawabi bayan da ya gana da shugaba Buhari.
Yayin da jerin gwanon motocin shugaban kasar ke kan hanyarsu ta zuwa fadar Aso Rock daga filin jirgin sama na Abuja, magoya bayan shugaban kasar sun jeru a gefunan tituna suna fadin “Baba Oyoyo”.
Buhari da kansa ya umarci jerin gwanon motocin kan su tsaya domin karbar gaisuwar da ake masa.
Da yake magana kan wannan Osinbajo, yace da yawa daga cikin mutanen sun samu rahoton dawowar shugaban kasar sa’o’i kadan da suka wuce amma duk da haka sukayi jerin gwano a gefen titin suna yiwa shugaban sannu da zuwa.
Osinbajo ya kara da cewa warkewar Buhari daga rashin lafiyar da yayi fama da ita na nuna cewa kasarnan zata fita daga matsalar da take ciki.