An gano wani gida a jihar Lagos da wasu mutane da ba’asan ko su waye ba ke amfani dashi wajen yin garkuwa da mutane a yankin Ile-Zik kusa da Ikeja babban birnin jihar.
Jami’an tsaro da suka bincike gurin sun gano wasu sassan jikin biladama a gidan.
An kuma gano hanyoyin karkashin kasa da dama a yankin dake kusa da filin jirgin sama na Murtala Muhammad.
An dai gano wurin ajiye mutanen ne bayan da wata mai talla da aka sace kuma ta samu ta kubuta, ta an karar da mutane abinda yake faruwa a gurin.
Mutanen dake zaune kusa da wurin sun mamaye gidan inda aka gano takalman mutane maza da mata da sauran kayayyaki da dama.
Mutane uku aka kama, yayin da aka kama mutum na hudu da wuka a hannunsa wanda yayi shigar burtu a zuwan mahaukaci ne.
Wani dan sanda ya shaidawa jaridar The Cable cewa mutanen na can na amsa tambayoyi a ofishin yan sanda na Isokoko dake yankin Agege