Rundunar yan sandan jihar Yobe, ta kama wasu jami’an hukumar aikin hajji ta jihar da kuma wasu ma’aikatan karamar hukumar Potiskum kan zargin bacewar kudin aikin hajji na wasu maniyata 41.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Jafiya Zubairu, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na NAN kama mutanen yau Alhamis a birnin Damaturu.
A cewarsa jami’an gwamnatin sun karkatar da kudaden ajiyar maniyata 41 da suka fito daga karamar hukumar Potiskum, inda suka gaza sama musu takardun tafiya.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan yace tuni sashin binciken manyan laifuka na rundunar ya kaddamar da bincike akan lamarin.
” Amma kuma bazan iya bayyana adadin mutanen da abin ya rutsa dasu ba, saboda ana cigaba da bincike,” yace.
NAN ya rawaito cewa maniyata 41 da abin ya shafa sun gudanar da zanga-zanga a majalisar dokokin jihar domin neman saka bakin majalisar don su samu suyi aikin hajjin bana.
Alhaji Adamu Dala-Dogo, shugaban majalisar ya tabbatarwa da maniyatan cewa majalisar zata hada kai da bangaren zartarwa don ganin cewa sun sauke farali.