Majalisar dattawa a ranar Talata tace shugaban kasa Muhammad Buhari bai saba Ko wacce doka ba kan kin dawowa gida da yayi daga birnin London inda yake jiya.
Majalisar dattawan ta bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Aliyu Abdullah yafitar.
Majalisar na maida martani ne kan zanga-zangar da wasu kungiyoyin fararen hula suke inda suke bukatar shugaban kasa yayi murabus saboda tsawon lokacin da ya shafe yana jinya a birnin London.
Sun shawarci masu zanga-zangar da su daina kawo rudani a kasa.
Majalisar dattawan tace zanga-zangar wani shiri ne na karkatar da hankalin fadar shugaban kasa daga kan tattalin arziki da kuma harkar tsaro wanda tuni an samu nasarar akan su.
Buhari ya bi tanadin kundin tsarin mulki shekarar 1999, inda a ciki aka bayyana cewa dole ne ya danka mulki a hannun mataimakinsa kana ya sanar da dukkanin majalisun kasa biyu akan tafiyarsa zuwa duba lafiyarsa.
” Shugaban kasa bai karya wata doka ba saboda haka ba muga dalilin wannan karkatar da hankali da kuma surutu ba, wadanda suka dau nauyin abun kawai suna neman suna ne,”yace.