Monday, 7 August 2017

News:Wanda Ya Kai Hari Kan Coci A Anambra Na Magana Ne Da Harshen Igbo

Tags




Garba Umar, Kwamishinan yan sandan jihar Anambra ya musalta rade-radin  da ake yadawa cewa yan Kungiyar Boko Haram ne suka kai hari kan Cocin Katolika da ake kira S.t Philip a karamar hukumar Ekwusigo dake jihar.

Da yake magana da manema labarai bayan da ya ziyarci wurin da abin ya faru,Umar yace  binciken da suka gudanar ya nuna cewa maharan suna  magana da yaren Igbo lokacin da suka kai harin.Yan bindiga sun mamayen Cocin lokacin da ake gudanar da addu’ar safe inda suka bude wuta kan masu ibada.

A kalla mutane takwas ne suka mutu nan take yayin da 18 suka samu munanan raunuka.

Umar yace yan asalin yankin ne suka kai harin.

Yakara da cewa an ajiye gawarwakin mutanen a asibitin koyarwa na jami’ar Nmandi Azikiwe dake Nnewi.

” Daga binciken da mukayi , a zahiri yake cewa mutumin da yakai harin dole ne ya zama dan asalin yankin, ” yace.

” Mutumin bayan ya kashe mutumin da yake nema ya cigaba da harbi inda ya kashe masu ibada da dama.

“Bayanin dake gaban yan sanda yanuna cewa maharin yana magana ne da yaren Igbo lokacin da yake harbi kan masu ibadar. ”

 Umar yace duk da ba a kama kowa ba kan harin amma yan sanda sun gano cewa harin na da alaka da wasu yan yankin Ozubulu dake zaune a kasar waje.