Friday, 11 August 2017

News:Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kai Hari A Adamawa Inda Suka Kona Gidaje 60

Tags




A kalla gidaje 60 aka kona a wani sabon hari da kungiyar yan ta’addar Boko Haram ta kai akan al’ummar Ghumbili dake karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.

Harin yana zuwa ne kwanaki biyu bayan da aka kai makamancin sa akan wani kauye kusa da garin na Ghumbili inda maharan suka kashe mutane 7.

Yusif Muhammad,shugaban karamar hukumar Madagali yace maharan sun shafe awanni hudu suna barna a garin.

Ya kuma ce yan kungiyar sun kwashe kayayyakin abinci da dama.

 “Sun sace kayan abinci, suka kashe dabbobi kana suka kona ga baki dayan kauyen,” yace.

 Muhammad,yace  har yanzu babu cikakken adadin mutanen da suka mutu ko kuma suka samu raunuka a harin,mutanen da suka tsira da ga harin yanzu haka sun nemi mafaka a garin Gulak hedikwatar karamar hukumar.

Othman Abubakar kakakin rundunar yan sandan jihar Adamawa ya tabbatar da faruwar harin sai dai yace babu wanda ya rasa ransa a harin.amma kuma ya tabbatar da an kona gidaje da dama.