Dan shekara 23,Ayobami Adedeji da ake zargi da aikata fashi da makami wanda yan sanda suka kama a yankin Alagbado dake Lagos a karshen makon da ya gabata yace ya shiga sana’ar sata ne saboda kada yunwa ta kashe shi.
Yan sanda dake sintiri ne suka kama mai laifin da misalin karfe 10:00 bayan da ya kwace jaka a hannun wata mata a wurin hawa da sauka daga mota da ake kira Kola dake yankin Alagbado.
An gano cewa mutumin da ake zargi da aikata laifin tare da wani da ake nema ruwa a jallo, sun samu nasarar kwace jakun kuna biyu lokacin da suke kokarin kwace ta ukun ne yayin da suke kan babur yan sanda suka bisu inda suka samu nasarar kama daya daga cikinsu.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Lagos, Olarinde Famous-Cole, wanda ya tabbatar da kama mai laifin yace Adedeji shi da abokin aikinsa da yake kira da Aboki suna amfani da babur ne wajen aikata sana’arsu, a ranar Litinin sun kwace jaka a hannun wata mata Kudirat Oyebode
Cole ya kara da cewa mai tuka babur din ya samu nasarar tserewa yabar babur din yayin da aka kama Adedeji da bindiga a tare dashi.
A jawabin da yayiwa yan sanda Adedeji yace shi karen mota ne ada.
Ya kuma ce wannan ne karon su na farko da suka aikata irin wannan laifi,kuma sunyi haka ne domin su samu na cin abinci.