Charley Boy, mawaki kuma mai fafutuka ya fadi kasa bayan da ya shaki hayaki mai sa hawaye bayan da jami’an yan sandan kwantar da tarzoma suka har ba musu barkonon tsohuwa.
Yan sandan kuma sun fesa ruwa mai karfi akan masu zanga-zangar wadanda suke bukatar Buhari,ya dawo aiki ko kuma ya sauka daga mulki.
Buhari yana can birnin London inda likitoci suke kula da lafiyarsa tun ranar 7 ga watan Mayu sama da kwanaki 90 kenan.
A ranar Litinin wasu kungiyoyin fararen hula sun fantsama kan tituna suna bukatar shugaban kasar ya koma aiki ko kuma ya sauka daga mulki.
Kungiyar sun ci alwashin cigaba da zanga-zangar tasu a dandalin da ake kira Unity Fountain dake Abuja har sai Buhari ya dawo ko kuma ya sauka daga mulki.
Cikakken bukatum kungiyar dai sune ; ” Shugaban kasa da kansa ko kuma ta hannun wani mai taimaka masa ya bayyanawa yan Najeriya cikakken halin da lafiyarsa ke ciki, shugaban kasar yayi wa yan Najeriya jawabi a yaren da kowa yake ji da za mu iya fahimtar halin lafiyarsa, ya dawo Najeriya ya cigaba da shugabanci a matsayin kwamandan askarawan sojin Najeriya domin ya fitar damu daga matsalar tattalin arziki da matsalar tsaro da ake fama dasu. ”
An dai gudanar da zanga-zangar lafiya a ranar Litinin.
Amma a ranar Talata yan sanda sunyi amfani da karfin tuwo wajen watsa masu zanga-zangar.