Sunday, 20 August 2017

Mun Gode Allah Da Ya Bawa Buhari Lafiya, A cewar PDP


Jam’iyar PDP ta bayyana cewa tunda  ya dawo daga jinya a birnin London, yanzu shugaban kasa Muhammad Buhari, yana da cikakkiyar lafiyar da zai iya jagorancin Najeriya.

 Buhari ya dawo Najeriya a ranar Asabar, bayan da yabar gida tun ranar 7 ga watan Mayu don yin jinya a birnin London.

 A wata sanarwa da mai magana da yawun PDP na kasa Dayo Adeyeye,   yafitar, jam’iyar tayi murna da dawowar shugaban  kasar ta kuma godewa Allah da yabashi lafiya.

 Ta kuma yi addu’ar Allah yakarawa shugaban kasar lafiya domin ya fitar da tattalin arzikin Najeriya daga mawuyacin halin da yake ciki.

 ” Muna da yakinin cewa yanzu mai girma shugaban kasa yana da cikakkiyar lafiyar cigaba da gudanar da aikinsa a matsayinsa na shugaba,” sanarwar tace.

“Mun godewa Allah da ya ceci rayuwarsa.

“Muna addu’ar Allah yakara masa lafiya da kuma fahimtar yadda zai ceto tattalin arzikin mu daga mawuyacin  halin da yake ciki da kuma kawowa yan Najeriya saukin wahalhalun da suke fuskanta.”

Mutane Da Yawa Suna Farin Cikin Dawowar Buhari – Osinbajo


Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo,yace yan Najeriya da yawa suna farin ciki da dawowar shugaban kasa Muhammad Buhari.

Ya fadi haka ne lokacin da yakewa yan jaridun fadar shugaban kasa jawabi  bayan da ya gana da shugaba Buhari.

 Yayin da jerin gwanon motocin shugaban kasar ke kan hanyarsu ta zuwa fadar Aso Rock daga filin jirgin sama na Abuja,  magoya bayan shugaban kasar sun jeru a gefunan tituna suna fadin “Baba Oyoyo”.

Buhari da kansa ya umarci jerin gwanon motocin kan su tsaya domin karbar gaisuwar da ake masa.

Da yake  magana kan wannan Osinbajo, yace da yawa daga cikin mutanen sun samu rahoton dawowar shugaban kasar sa’o’i kadan da suka wuce amma duk da haka sukayi jerin gwano a gefen titin suna yiwa shugaban sannu da zuwa.

 Osinbajo ya kara da cewa warkewar Buhari daga rashin lafiyar da yayi fama da ita na nuna cewa kasarnan zata fita daga matsalar da take ciki.

Yan Sanda Sun Kama Yan Jaridar Bogi Su Biyar


Rundunar yan sandan Najeriya  ta bayyan kama wasu mutane biyar wadanda suke bayyana kansu a matsayin  yan jarida domin samun damar shiga wurin taro inda suke amfani da damar wajen tabka sata a wurin manyan mutane.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Jimoh Mashood,  yafitar tace wadanda aka kama sun hada da shugabansu,Musa Auwalu dan shekara 43  daga Kano, Kolawole  Akinbode mai shekaru 50 daga Ogun  da kuma Umar Abba  dan shekara 53 daga Adamawa.

Har ila yau an kama Abdullahi Muhammad mai shekaru 50 daga  Bauchi da kuma Muhammad Sale mai shekaru 60 daga jihar Kano.

Sanarwar tace an kama mutanen da ake zargi a jihohin Kano, Ogun, Edo da kuma birnin tarayya Abuja.

Mista Mashood ya lissafa kayayyakin da aka gano a hannun mutanen da ake zargi da suka hada da wayoyin hannu 13, katin shedar bogi na kafafen yada labaran da babu su, da kuma gida a Kano wanda Auwalu ya gina.

“An kama mutanen ne bayan da bangaren rundunar na musamman ya karbi korafin satar wayar wani babban mutum lokacin da ya halarci biki a Abeokuta dake jihar Ogun ranar 6 ga watan Yuli,daganan rundunar tabi sawun masu laifin kuma suka samu nasarar kama su.

” An gano  gidan da Auwalu ya gina a Kano da kudin kayan satar da suka siyar,” Mashood yace.

Saturday, 19 August 2017

Daga Zauren FIQHU: Yadda Ake Warware Sihiri A Musulunci


Za a  fara ne da yin  alwala tare da rokon Allah da siffofinSa daga nan sai a karanta wadannan Ayoyin AlKur’ani a bayyane akan wanda aka yi wa Sihirin;

1) Ayatul Kursiyyu ( Suratul Bakara: Aya ta 255

2) Shahidallahu ( Suratul Imran: Aya ta 18

Daga nan sai a nemi ganyen Magarya kunne bakwai, a dan daka su da Dutse sannan a saba dandakakken ganyen da ruwa, sai a zuba cikin bukitin wanka. Daga nan sai a karanta wadannan Ayoyin AlKur’ani a cikin ruwan;

* A’uzubillahi Minas Shaidanin Rajim

* Ayatul Kursiyyu

* ‘ Wa’auhaina,,,,,” Suratul A’araf: Aya ta 110 zuwa 117

* ” Wakala Fir’auna…” Suratul Yunus: Aya ta 79 zuwa 82

* ” Kalu ya Musa….” Suratul Daha: Aya ta 65 zuwa 70

* Suratul Kafirun

* Suratul Ikhlas

* Suratul Falak

* Suratul Nas

* Sai a karanta ” La’ilaha Illallahu Wahdahu Lasharikalahu Lahul Mulku Walahulhamdu Wahuwa Ala Kulli Shai’in Kasiri” ( Sau Dari). Sai a kammala da Salatin Manzon Allah ( SAW)

 Daga sai a dibi ruwan a ba mara lafiyan ya sha sai kuma ya yi wanka da sauran ruwan.
Allah ne mafi sani.

News:Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Dawo Gida Nijeriya A Safiyar Yau

Muna Taya Shugaba Buhari Barka Da Dawowa Kasa Najeriya.

Ana Sa Ran zai yi magana da yan Najeriya ranar litinin 21 ga wata, da misalin karfe 7am na safe in Allah ya Yarda


Friday, 18 August 2017

News:Wani Mutum Yayiwa ‘Yar Shekara 6 Fyade


Wani mutum Dan shekaru 20 Francis Yawu an gurfanar dashi a gaban kotu Surulere don yayiwa ‘yar Shekaru 6 Fyade.

Francis Yawu yana zaune a titin Zamba Itire jahar Legas, dan sandan Sajan Anthonia Osayande ya bayyanawa kotu ya aikata laifinne a 17 ga watan Yuli.

Mai laifin dai suna Unguwa dayane da yarinyar amma Mai Shariar yabada Belinda akan kudi naira Miliyan 1 a kawo wasu manyan mutane 2

Thursday, 17 August 2017

Sport:Real Madrid Ta Doke Barcelona A Karo Na Biyu Na Gasar Super Cup


Real Madrid Ta Dauki Super Cup Na Kasar Spain, Bayan Ta Lallasa Barcelona Da Ci 2-0 A Wasa Zagaye Na Biyu


Kannywood:Yakubu Muhammad zagaye da mata a wani shirin fim din turanci


Jarumin fim din hausa, Yakubu Muhammad kena, zagaye da mata a wannan shirin fim dinnashi na turanci me suna matar makwaucina.

 Masoyanshi da dama sun nuna kwadayin ganin wannan shirin don ganin ya zata kaya.

Wednesday, 16 August 2017

Comedy:Download bush kiddo baka nike

Friday, 11 August 2017

News:Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kai Hari A Adamawa Inda Suka Kona Gidaje 60


A kalla gidaje 60 aka kona a wani sabon hari da kungiyar yan ta’addar Boko Haram ta kai akan al’ummar Ghumbili dake karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.

Harin yana zuwa ne kwanaki biyu bayan da aka kai makamancin sa akan wani kauye kusa da garin na Ghumbili inda maharan suka kashe mutane 7.

Yusif Muhammad,shugaban karamar hukumar Madagali yace maharan sun shafe awanni hudu suna barna a garin.

Ya kuma ce yan kungiyar sun kwashe kayayyakin abinci da dama.

 “Sun sace kayan abinci, suka kashe dabbobi kana suka kona ga baki dayan kauyen,” yace.

 Muhammad,yace  har yanzu babu cikakken adadin mutanen da suka mutu ko kuma suka samu raunuka a harin,mutanen da suka tsira da ga harin yanzu haka sun nemi mafaka a garin Gulak hedikwatar karamar hukumar.

Othman Abubakar kakakin rundunar yan sandan jihar Adamawa ya tabbatar da faruwar harin sai dai yace babu wanda ya rasa ransa a harin.amma kuma ya tabbatar da an kona gidaje da dama.

News:An Gano Maboyar Masu Garkuwa Da Mutane A Kusa Da Ikeja


An gano wani gida a jihar Lagos da wasu mutane da ba’asan ko su waye ba ke amfani dashi wajen yin garkuwa da mutane a yankin Ile-Zik kusa da Ikeja babban birnin jihar.

Jami’an tsaro da suka bincike gurin sun gano wasu sassan jikin biladama a gidan.

 An kuma gano hanyoyin karkashin kasa da dama a yankin dake kusa da filin jirgin sama na Murtala Muhammad.

An dai gano wurin ajiye mutanen ne bayan da wata mai talla da aka sace kuma ta samu ta kubuta, ta an karar da mutane abinda yake faruwa a gurin.


Mutanen dake zaune kusa da wurin sun mamaye gidan inda aka gano takalman mutane maza da mata  da sauran kayayyaki da dama.

Mutane uku aka kama, yayin da aka kama mutum na hudu da wuka a hannunsa wanda yayi shigar burtu a zuwan mahaukaci ne.

Wani dan sanda ya shaidawa jaridar The Cable cewa mutanen na can na amsa tambayoyi a ofishin yan sanda na Isokoko dake yankin Agege

News:An Kama Wasu Jami’an Hukumar Aiki Hajji Ta Jihar Yobe Da Laifin Sata


Rundunar yan sandan jihar Yobe, ta kama wasu jami’an hukumar aikin hajji ta jihar  da kuma wasu ma’aikatan karamar hukumar  Potiskum kan zargin bacewar kudin aikin hajji na  wasu maniyata 41.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Jafiya Zubairu, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na NAN kama mutanen yau Alhamis a birnin Damaturu.

  A cewarsa jami’an gwamnatin sun karkatar da kudaden ajiyar maniyata 41 da suka fito daga karamar hukumar Potiskum, inda suka gaza sama musu takardun tafiya.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan yace tuni sashin binciken manyan laifuka na rundunar ya kaddamar da bincike akan lamarin.

” Amma kuma bazan iya bayyana adadin mutanen da abin ya rutsa dasu ba, saboda ana cigaba da bincike,” yace.

NAN ya rawaito cewa maniyata 41 da abin ya shafa sun gudanar da zanga-zanga a majalisar dokokin jihar domin neman saka bakin majalisar don su samu suyi aikin hajjin bana.

Alhaji Adamu Dala-Dogo, shugaban majalisar ya tabbatarwa da maniyatan cewa majalisar zata hada kai da bangaren zartarwa don ganin cewa sun sauke farali.

Wednesday, 9 August 2017

News:Yan Sanda A Zaria Sun Kama Wanda Yayi Garkuwa Da Wani Injiniya Dan Kasar China


Yan sanda sun kama daya daga cikin mutanen da sukayi garkuwa da wani Injiniya dan kasar China dake aiki a kamfanin dake aikin samar da ruwa a garin Zaria.

 Zhang Lijun wanda yake aiki da kamfanin gine-gine na CGC an sace shine a ranar Litinin a kauyen Dakace dake wajen Zaria  akan hanyar Jos, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa wajen aiki.

 Da yake tabbatar da kama mutumin kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, ASP Yakubu Sabo yace yan sanda sun samu nasarar ceto mutumin tare da kwato wasu kayayyaki daga wadanda ake zargi da garkuwa da shi. 

Saboda haka yayi kira ga maigidanta da su cigaba da taimakawa yan sanda da bayanai daza su taimaka wajen maganin garkuwa da mutane da kuma sauran laifuka a jihar.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta fadawa jaridar Daily Trust yadda aka yi garkuwa da Liju “Yana tare da direbansa,Haruna Muhammad lokacin da wasu mutane biyu suka kai musu hari da bindiga, suka jefar da direbansa da sukayi awon gaba da Lijun,” a cewar majiyar.

 Mutumin da ake zargi da garkuwar  Paul Ochalla daga jihar Rivers da kuma daya mutumin daga jihar Akwa Ibom wanda ake nema, sun yi kokarin guduwa da mutumin amma basu yi nasara ba.

News:Majalisar Dattawa Ta Ce Buhari Bai Karya Doka Ba Kan Tafiya Jinya Da Yayi


Majalisar dattawa a ranar Talata tace shugaban kasa Muhammad Buhari bai saba Ko wacce doka ba kan kin dawowa gida da yayi daga birnin London inda yake jiya.

Majalisar dattawan  ta bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Aliyu Abdullah yafitar.

Majalisar na maida martani ne kan zanga-zangar da wasu kungiyoyin fararen hula  suke inda suke bukatar shugaban kasa yayi murabus saboda tsawon lokacin da ya shafe yana jinya a birnin London.

Sun shawarci masu zanga-zangar da su daina kawo rudani a kasa.

Majalisar dattawan tace zanga-zangar wani shiri ne na karkatar da hankalin fadar shugaban kasa daga kan tattalin arziki da kuma harkar tsaro wanda tuni an samu nasarar akan su.

Buhari ya bi tanadin kundin tsarin mulki shekarar 1999, inda a ciki aka bayyana cewa dole ne ya danka mulki a hannun mataimakinsa kana ya sanar da dukkanin majalisun kasa biyu akan tafiyarsa zuwa duba lafiyarsa.

” Shugaban kasa bai karya wata doka ba saboda haka ba muga dalilin wannan karkatar da hankali da kuma surutu ba, wadanda suka dau nauyin abun kawai suna neman suna ne,”yace.

News:Charley Boy Ya Fadi Lokacin Da Suke Tsaka Da Zanga-Zangar Neman Buhari Ya Sauka


Charley Boy, mawaki kuma mai fafutuka ya fadi kasa bayan da ya shaki hayaki mai sa hawaye bayan da jami’an yan sandan kwantar da tarzoma suka har ba musu barkonon tsohuwa.

Yan sandan kuma sun fesa ruwa mai karfi akan masu zanga-zangar wadanda suke bukatar Buhari,ya dawo aiki ko kuma ya sauka daga mulki.

Buhari yana can birnin London inda likitoci suke kula da lafiyarsa tun ranar 7 ga watan Mayu sama da kwanaki 90 kenan.

A ranar Litinin wasu kungiyoyin fararen hula sun fantsama kan tituna suna bukatar shugaban kasar ya koma aiki  ko kuma ya sauka daga mulki.

Kungiyar sun ci alwashin cigaba da  zanga-zangar tasu a dandalin da ake kira Unity Fountain dake Abuja har sai Buhari ya dawo ko kuma ya sauka daga mulki.

 Cikakken bukatum kungiyar dai sune ; ” Shugaban kasa da kansa ko kuma ta hannun wani mai taimaka masa ya bayyanawa yan Najeriya cikakken halin da lafiyarsa ke ciki, shugaban kasar yayi wa yan Najeriya jawabi a yaren da kowa yake ji da za mu iya fahimtar halin lafiyarsa, ya dawo Najeriya ya cigaba da shugabanci a matsayin kwamandan askarawan sojin Najeriya  domin ya fitar damu daga matsalar tattalin arziki da matsalar tsaro da ake fama dasu. ”

An dai gudanar da zanga-zangar lafiya a ranar Litinin.

Amma a ranar Talata yan sanda sunyi amfani da karfin tuwo wajen watsa masu zanga-zangar.

Monday, 7 August 2017

News:Babu Maganar Chanja Shugaba Buhari- Lai Muhammed



Ministan Labarai Lai Muhammed yace ba Wanda zai chanji Buhari saboda Gwamnatin Najeriya na tafiya yadda yakamata tun bayan tafiyar Muhammadu Buhari wajen duba lafiyarsa.

Shugaba Buhari kwanansa 90 a birnin Landan kenan wajen duba lafiyarsa, Lai Muhammed yace ba Wanda baya rashin Lafiya sannan Shugaba Buhari yana samun Lafiya, sannan ya kara da cewa Shugaba Muhammad Buhari na daf da Dawowa.

News:Ban Tsani Fulani Ba Ko Wani- Fayose


bayani a shafukan sadarwarsa cewa bai Tsani Fulani ba ko wani kawai shi kawai bayason anawa manoma barna a gonakinsu.

Gwamna Fayose ya shawarci makiyaya dasu tsaftace sana’arsu basai sun dinga barnata gonakin Manoma ba

Images:Dubi Irin Gidan Da Gwamnan Jihar Kogi Ya Gina A Abuja

An gurfanar da Johnson Musa a gaban Alkalin Birnin Lokoja saboda ya tona asirin Katafaren Gidan da Gwamna Yahaya Bello ya mallaka a birnin tarayya Abuja Wanda kudinsa yakai kimanin Naira biliyan 2.1, Gidan dai yana Asokoro.


Images:Hotunan Katafaren Gidan Ibrahim Badamasi Babangida Dake Minna






News:Yunwa Ce Ta Sa Ni Aikata Fashi Da Makami


Dan shekara 23,Ayobami Adedeji  da ake zargi da aikata fashi da makami wanda yan sanda suka kama a yankin Alagbado dake Lagos  a karshen makon da ya gabata yace ya shiga sana’ar sata ne saboda kada yunwa ta kashe shi.

Yan sanda dake sintiri ne suka kama mai laifin  da misalin karfe 10:00 bayan da ya kwace  jaka a hannun wata mata a wurin hawa da sauka daga mota da ake kira Kola dake yankin Alagbado.

An gano cewa mutumin da ake zargi da aikata laifin tare da wani da ake nema ruwa a jallo, sun samu nasarar kwace jakun kuna biyu lokacin da suke kokarin kwace ta ukun ne yayin da suke kan babur yan sanda suka bisu inda suka samu nasarar kama daya daga cikinsu.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Lagos, Olarinde Famous-Cole, wanda ya tabbatar da kama mai laifin yace Adedeji shi da abokin aikinsa da yake kira da Aboki  suna amfani da babur ne  wajen aikata sana’arsu, a ranar Litinin sun kwace jaka a hannun wata mata Kudirat Oyebode

Cole ya kara da cewa mai tuka babur din ya samu nasarar tserewa yabar babur din yayin da aka kama Adedeji da bindiga a tare dashi.

A jawabin da yayiwa yan sanda Adedeji yace shi karen mota ne ada.

 Ya kuma ce wannan ne karon su na farko da suka aikata irin wannan laifi,kuma sunyi haka ne domin su samu na cin abinci.

News:Wanda Ya Kai Hari Kan Coci A Anambra Na Magana Ne Da Harshen Igbo


Garba Umar, Kwamishinan yan sandan jihar Anambra ya musalta rade-radin  da ake yadawa cewa yan Kungiyar Boko Haram ne suka kai hari kan Cocin Katolika da ake kira S.t Philip a karamar hukumar Ekwusigo dake jihar.

Da yake magana da manema labarai bayan da ya ziyarci wurin da abin ya faru,Umar yace  binciken da suka gudanar ya nuna cewa maharan suna  magana da yaren Igbo lokacin da suka kai harin.Yan bindiga sun mamayen Cocin lokacin da ake gudanar da addu’ar safe inda suka bude wuta kan masu ibada.

A kalla mutane takwas ne suka mutu nan take yayin da 18 suka samu munanan raunuka.

Umar yace yan asalin yankin ne suka kai harin.

Yakara da cewa an ajiye gawarwakin mutanen a asibitin koyarwa na jami’ar Nmandi Azikiwe dake Nnewi.

” Daga binciken da mukayi , a zahiri yake cewa mutumin da yakai harin dole ne ya zama dan asalin yankin, ” yace.

” Mutumin bayan ya kashe mutumin da yake nema ya cigaba da harbi inda ya kashe masu ibada da dama.

“Bayanin dake gaban yan sanda yanuna cewa maharin yana magana ne da yaren Igbo lokacin da yake harbi kan masu ibadar. ”

 Umar yace duk da ba a kama kowa ba kan harin amma yan sanda sun gano cewa harin na da alaka da wasu yan yankin Ozubulu dake zaune a kasar waje.

News:Buhari Yayi Allah Wadai Da Harin Da Wasu Yan Bindiga Suka Kai Wata Coci A Anambra


Shugaban kasa Muhammad Buhari yayi Allah wadai da harin da aka kai wata majami’a dake jihar Anambra.

Buhari a wata sanarwa da yafitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu, ya bayyana harin a matsayin a wani abu mai muni da bai dace ba akan bil’ama.

Shugaban kasar ya bayyana damuwar kai harin, inda yace ” Babu wani dalili kowanne iri da zai sa akai hari  kan masu Ibada cikin cocin tare da kashe su cikin ruwan sanyi.”

 Shugaban ya jajantawa iyalan wadanda suka rayukansu, shugabannin cocin da kuma gwamnatin jihar Anambra.

Ya kuma tabbatarwa da yan Najeriya kokarin gwamnatinsa na kare dukiyoyinsu da rayukansu a koda yaushe kuma a ko ina suke.

News:Sojoji Sun Kashe Yan Kungiyar Boko Haram 13


Sojojin da suke aiki karkashin shirin samar da tsaro a yankin arewa maso gabas da ake kira Operation Lafiya Dole, sun kashe yan kungiyar Boko Haram a sama da 13 a  yankuna daban-daban  na jihohin Adamawa da Borno.

Mai magana da yawun rundunar sojin Birgediya Janar Sani Usman,ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar  inda yace an kashe yan kungiyar 12 a wani harin kwanton bauna da sojoji suka kai musu a mahadar hanyar Miyanti-Banki dake Borno da kuma Kafin Hausa a Madagali dake jihar Adamawa.

Usman yakara da cewa an kashe wasu yan kungiyar da dama a kan hanyar Dukje-Mada  kusa da kauyen Gulumba gana.

” Amma abin takaici sojoji biyu sun rasa rayukansu lokacin da motar da suke ciki ta taka nakiya da aka binne akan hanya,yayin da guda hudu suka samu raunuka.

“An an dawo  da gawarwakin jajirtattum sojojin da suka mutu  da kuma wadanda suka jikkata birnin Maiduguri, ” Usman yace.

Ya lissafa kayayyakin da aka kwato daga hannun yan ta’addar da suka hada da keken hawa 18, buhun fulawa 30,buhun gyada daya, buhun gishiri,bandir din yadi, huhun goro guda biyu, tocilan da kuma sauran kayayyaki.

Sunday, 6 August 2017

Music:whimz Energy new hot song


Facebook :whimz_c.
Twitter :whimz_c.
Instagram: whimz_c

Download here

Bollywood:Fim Din Shah Rukh Khan Jab Harry Met Sejal Ya Fito



Fim din shahararren jarumin nan na Bollywood, Shah Rukh Khan, da Anushka Sharma, mai suna Jab Harry Met Sejal, da aka dade ana jira ya fito yau juma’a, a kasar Indiya, ana kuma sa ran cewa wannan fim din zai fito da sa’a domin ana harsashen cewa zai baiwa marada kunya .
Ana sa ran cewa a ranar farko fim din zai yi cikin fiye da dalar Amurka miliyan uku, hatta masu fashin baki akan harkokin kasuwanci a Indiya, kamar Akshaye Rathi, ya tabbatar da cewar daga dukkan alamu fim din zai yin kasuwan da ake zato.
Ya kara da cewa a ranar farko yana harsashen cewa gidajen kallo a kasar zasu cika makil masamman ma na birane wanda dama su ake hako.
Ganin cewa akwai fiye da gidajen kallo dubu uku (3,000) da za a iya amfani dasu domin gamsar da masu kallo haka shima zai taimaka wajan samun Karin kudaden shiga