Sunday, 20 August 2017

Yan Sanda Sun Kama Yan Jaridar Bogi Su Biyar

Tags




Rundunar yan sandan Najeriya  ta bayyan kama wasu mutane biyar wadanda suke bayyana kansu a matsayin  yan jarida domin samun damar shiga wurin taro inda suke amfani da damar wajen tabka sata a wurin manyan mutane.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Jimoh Mashood,  yafitar tace wadanda aka kama sun hada da shugabansu,Musa Auwalu dan shekara 43  daga Kano, Kolawole  Akinbode mai shekaru 50 daga Ogun  da kuma Umar Abba  dan shekara 53 daga Adamawa.

Har ila yau an kama Abdullahi Muhammad mai shekaru 50 daga  Bauchi da kuma Muhammad Sale mai shekaru 60 daga jihar Kano.

Sanarwar tace an kama mutanen da ake zargi a jihohin Kano, Ogun, Edo da kuma birnin tarayya Abuja.

Mista Mashood ya lissafa kayayyakin da aka gano a hannun mutanen da ake zargi da suka hada da wayoyin hannu 13, katin shedar bogi na kafafen yada labaran da babu su, da kuma gida a Kano wanda Auwalu ya gina.

“An kama mutanen ne bayan da bangaren rundunar na musamman ya karbi korafin satar wayar wani babban mutum lokacin da ya halarci biki a Abeokuta dake jihar Ogun ranar 6 ga watan Yuli,daganan rundunar tabi sawun masu laifin kuma suka samu nasarar kama su.

” An gano  gidan da Auwalu ya gina a Kano da kudin kayan satar da suka siyar,” Mashood yace.